- Musulman yan kwallon kafa sun tafi aikin Hajji
- Shima Kareem Benzema na daga cikin wadanda suka tafi yin bautan
Gwarzon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Kareem Benzema ya isa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajji na bana, inji rahoton jaridar Rariya.
Kareem Benzeman ya garzaya kasar Saudiyya ne bayan daya fafata a wasan da aka buga tsakanin Real Madrid da Valencia a ranar Lahadi data gabata.
KU KARANTA: Yansanda sun koka kan yawaitan yadda iyaye ke zakkewa ýaýansu a Kano
Saida majiyar Legit.ng tace ba wannan bane karo na farko da Benzema ke zuwa kasar Makkah da Madina ba don gudanar da Hajji ko Umrah ba.
Ko a karshen kakar data gabata, sai da shahararren dan wasan ya gudanar da ibadar Umarah a kasar Makkah, tare da wasu shahararrun yan wasa da suka hada da dan wasan Manchester Paul Pogba da na Chelsea Ngolo Kante.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kGtpcm5jYrWitsmipWaakaOubrTOraynmZ5iuKK%2BxJ6kZpqVo8emucBmsJqxmaN6pa3YmqKeZZeqsaK6wKtknZldlrastc1mn5qimp57qcDMpQ%3D%3D